31 Janairu 2022 - 19:21
​Mali: Takun Saka Na Dada Kamari Tsakanin Mahukunta Da Kuma Faransa

Ministan Harkokin wajen Mali ya bayyana cewar tsamin dangantakar dake tsakanin su da Faransa ya biyo bayan bijire wa manufofin kasar ne, sabanin jinkirta zaben shugaban kasar da ake matsa musu lamba akai.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ministan Abdoulaye Diop ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi ga Yan kasar Mali dake zama a Brussels, inda ya zargi Faransa da nuna son kai wajen sukar mulkin soji.

Diop yace Faransa wadda tace tana kare mulkin dimokiradiya taje wasu kasashe inda ta dora shugabanni da suka yi juyin mulkin na soji ta kuma jinjina musu.

Dangantaka tsakanin Mali da Faransa wadda ta yiwa kasar mulkin mallaka tayi kamari tun bayan juyin mulkin da soji suka yi a watan Agustan shekarar 2020.

Faransa na da dubban sojoji a kasar Mali wadanda ke rundunar yaki da Yan ta’adda a yankin Sahel.

Ana ci gaba da tankiya a kasar tun bayan takunkumin da ECOWAS ta dorawa Mali na karya tattalin arziki sakamakon juyin mulkin wanda ya samu goyan bayan Faransa da Amurka da kungiyar kasashen Turai.

Ministan harkokin wajen Faransa Jean Yves Le Drian ya bayyana gwamnatin sojin Mali a matsayin haramtacciya, inda ya zarge ta da kaucewa gudanar da zabe.

342/